Wani rahoto ya nuna cewa Najeriya ta haura zuwa matsayi na shida a jerin ƙasashen da suka fi fama da ta’addanci a duniya, daga matsayi na takwas a shekarun 2023 da 2024.
Rahoton, wanda aka fitar a ranar 5 ga Maris, ya bayyana Burkina Faso a matsayin ƙasa mafi fama da ta’addanci, sai Pakistan, Syria, Mali, da Jamhuriyar Nijar, kafin Najeriya.
Haka kuma, ƙasashen Somalia, Kamaru, da DR Congo na cikin jerin ƙasashe 13 da suka fi fuskantar hare-haren ta’addanci.
Rahoton ya ƙara da cewa Najeriya ta fuskanci kashe-kashe masu alaƙa da ta’addanci guda 565 a shekarar 2024.
