
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahir Muhammad Hashim ya bukaci dukkan Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati da ke jihar da su rika ware akalla kashi daya cikin dari (1%) na kasafin kudinsu domin yaki da sauyin yanayi.
Dakta Hashim ya bayyana haka ne a yayin wani taron tsara kasafin kudi na shekarar 2026 zuwa 2028 da aka gudanar a Kaduna, wanda Ma’aikatar Tsare-tsare da Kasafin Kudi ta jiar Kano ta shirya.
“Sauyin yanayi na kara zama barazana ga rayuwa da tattalin arziki da kuma muhalli, don haka akwai bukatar daukar matakan gaggawa, musamman a lokacin da ake fuskantar ambaliyar ruwa da fari da kuma sauran matsalolin da sauyin yanayi ke jawo wa”. In ji shi.
Kwamishinan ya kuma bukaci a dora muhimmanci kan ayyukan da za su taimaka wajen kare muhalli tare da inganta dabarun dorewar ci gaba a jihar.
Taron ya samu halartar mambobin Majalisar Zartarwa da ‘yan majalisa da daraktoci da kuma wakilan wasu kungiyoyin farar hula.