
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido ya bayyana cewa a shirye yake da ya shiga kowace haɗaka da nufin kawar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki a shekarar 2027.
Lamido ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a karshen mako.
Yayin da yake sukar gwamnatin Tinubu da zargin gazawa da rashin ƙwarewa, Lamido ya jaddada buƙatar kawar da jam’iyyar mai mulki ta APC daga mulki.
Fitaccen jigon jam’iyyar adawa ta PDP ya ce, a shirye yake ya shiga kowace irin ƙungiya ko haɗaka, matuƙar za a kawar da gwamnatin yanzu daga mulki.