
Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam’iyyun adawa a Najeriya sun shirya tsaf domin kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Atiku ya yi wannan bayani ne a ganawarsa da manema labarai a zauren taro na Yar’Adua Center da ke Abuja a ranar Alhamis.
A cewarsa, taron ya gudana ne domin samar da haɗin gwiwa tsakanin manyan ’yan adawa kafin babban zaɓe mai zuwa.
Tun bayan faduwar Atiku a zaɓen 2023, ya ci gaba da jagorantar tarurruka da shugabannin adawa, yana kokarin ƙarfafa ƙungiyoyin siyasa domin ganin an karɓe mulki daga hannun jam’iyyar APC.
A yayin taron, Atiku ya zargi Shugaba Tinubu da nuna son zuciya, yana mai cewa adawa za ta yi amfani da doka da tsarin dimokuraɗiyya wajen tabbatar da cewa an kawo sauyi a 2027.

A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas, wanda ya kai ga tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, tare da mataimakiyarsa da kuma ’yan majalisar dokokin jihar.
Wannan mataki ya haddasa martani daga manyan ’yan adawa, wadanda suka bayyana hakan a matsayin cin zarafin dimokuraɗiyya.
Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa, ciki har da Peter Obi (wakilcin Yunusa Tanko), Babachir Lawal, Nasir El-Rufai, Peter Ameh, da sauransu.