Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada a Jihar Kano, Hon. Ado Doguwa, ya bukaci a rufe Majalisar Tarayya tare da ayyana dokar ta-baci ta bangaren majalisa, har sai an dauki matakan da suka dace domin magance matsalar tsaro da ke addabar kasar nan.
Doguwa, wanda mamba ne a jam’iyyar APC mai mulki, ya bayyana hakan ne yayin zaman Majalisar Wakilai, inda ya ce duk da kokarin da gwamnati da hukumomin tsaro ke yi, har yanzu abin da ake yi bai kai yadda ya kamata ba.
“Ni dan APC ne, kuma ina magana ne a matsayina na dan jam’iyya mai mulki. Ina goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, amma dole ne mu fadi gaskiya. Gwamnati na kokari, amma kokarin bai isa ba,” in ji shi.
Ya bayyana halin tsaro a kasa a matsayin mai tayar da hankali da firgici, musamman a yankin Arewa.
“Halın tsaro a yau abin tsoro ne. Abin takaici ne. A wasu wurare kamar ana cikin yaki ne. Mutane na rayuwa cikin tsoro da fargaba. Manoma ba sa iya zuwa gona, ‘yan kasuwa ba sa iya zuwa kasuwa, masu ibada ba sa iya zuwa masallatai da coci-coci,” .
- Matsalar Tsaro: Alhassan Ado Doguwa ya bukaci a rufe majalisar wakilai
- A sake dawo da shari’ar zargin kisa da ake yiwa Ado Doguwa – Lauyoyi
Doguwa ya jaddada cewa babban aikin kowace gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a, yana mai cewa idan gwamnati ba ta iya yin hakan ba, dole ne a dauki mataki mai tsauri.
“Idan kasar nan na tafiya cikin jini, hawaye na kwarara, me muke zaune a nan muna tsarawa? Wa muke yi wa doka?” ya tambaya.
Ya kuma bukaci Majalisar da ta dubi kanta a matsayin wani bangare na gwamnati, ba wai ta jingina komai ga bangaren zartarwa kadai ba.
“Mu ma bangare ne na gwamnati. Idan akwai gazawa, dole mu duba kanmu. Za mu iya ayyana dokar ta-baci ta bangaren majalisa. Mu rufe Majalisar har sai an dauki matakin da ya dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a,” in ji Doguwa.
Dan majalisar ya kuma bayyana cewa mazabarsa ta Doguwa/Tudun Wada na fuskantar matsananciyar matsalar sace-sace da garkuwa da mutane, inda ya kwatanta yawaitar garkuwa da mutane da yadda ake shan magani a rana.
“A mazabata, garkuwa da mutane ya zama kamar yadda likita zai rubuta maka magani ka sha sau uku a rana – safe, rana da dare,” ya fada.
Sai dai duk da sukar da ya yi, Doguwa ya ce bai rasa fata da kudurin gwamnatin APC ba.
“Har yanzu ina da yakini da manufar ‘Renewed Hope’. Ina nan daram a APC, amma dole ne mu fadi gaskiya domin ceto kasar nan,” in ji shi.
Jawabin nasa ya jawo ce-ce-ku-ce a zauren Majalisar, inda wasu mambobi suka nuna goyon baya ga kiran a dauki mataki mai tsauri domin dakile matsalar tsaro da ke addabar kasar.
