Babban hafsan tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce mayaƙan Boko Haram da iyalansu 129,417 ne suka miƙa wuya a tsakanin 10 ga Yuli zuwa 9 ga Disamban 2024.
Musa, ya bayyana hakan ne a wani taron ƙasashen Afirka mai alaƙa da tsaro da ke gudana a Doha babban birnin Qatar.
Ya ce nasarar nada alaqa da goyan bayan da suke samu, wanda ke taka rawar ta samun nasara.
Ba sabon abu ne yadda rikicin Boko Haram ya daɗe yana cin kashe mutane, musammn a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Sai dai zuwa yanzu haka rundunar sojin na ci gaba da bayyana irin nasarorin da take samu kan mayaƙan na Boko Haram.
