Ahmad Hamisu Gwale
Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, ta sanar da kasashen Morocco, Portugal da Sifaniya a wadanda zasu karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2030.
A karo na biyu kenan da yankin nahiyar afrika zai sake karbar bakuncin gasar bayan a shekarar 2010 da kasar Afrika ta kudu ta karbi bakuncin gasar da Sifaniya ta lashe.
Haka zalika hukumar ta FIFA ta sanar da kasar Saudi Arabia a matsayin kasar da zata karbi bakuncin gasar da za ayi a shekarar 2034.
FIFA ta sanar da hakan ne a wani taron da hukumar ta gudanar a wannan Larabar bayan kammala kada kuria.
Ana saran za a buga wasanni uku a kasashen Argentina da Paraguay da Uruguay na gasar ta 2030 a matsayin bikin cikar gasar shekara 100 da farawa.
Duka mambobin FIFA 211 sun halarci taron da aka yi ta bidiyo, kuma sun kada luri’unsu ta hanyar yin tafi daga allon da ke nuna fuskokinsu.
Kasar Morocco wadda take daga yankin arewacin Afrika, tana kusa da kasashen na Sifaniya da kuma Portugal wadanda suka fito daga nahiyar turai.
Gasar ta shekarar 2026 dai za ta gudana a kasashe Uku da suka hadar America, Mexico da kuma Canada.