
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gaggauta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, tana mai nuna damuwa kan yadda tashin hankalin da ke gudana a Gaza ke ƙara jefa Falasɗinawa cikin mummunar hali.
Shugaban Majalisar António Guterres ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce rikicin ya zama babbar barazana ga rayuwar al’umar Falasɗinu, yana kuma haifar da bala’in jin ƙai da rashin tsaro.
Guterres ya kuma ce, ko da yake an fara kai ɗan agajin jin ƙai zuwa Gaza, hakan bai wadatar ba domin ana buƙatar daukar gaggawar mataki don kawo ƙarshen rikicin da ya durkusar da rayuwar miliyoyin jama’a.
Sanarwar ta Majalisar Dinkin Duniya ta zo ne awanni kaɗan bayan da hukumomin lafiya a Gaza suka tabbatar da mutuwar Falasɗinawa 14 cikin yini guda sakamakon yunwa da ƙalubalen rashin abinci da magunguna.