
Kungiyar Masu Gidajen Sayar Da Man Fetur A Najeriya (PETROAN), ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Hukumomin Kula Da Harkokin Mai, (NMDPRA) da su dakatar da shirin Matatar Dangote na rarraba Man fetur da Dizal ga gidajen mai a fadin kasar nan kai-tsaye.
Shugaban Kungiyar, Billy Gillis-Harry, ya bukaci hakan ne yayin hirarsa da Gidan Talabijin na Channels a farko makon nan.
Shugaban kungiyar ya ce, matakin rarraba Man kai-tsaye na iya jefa dubban ma’aikata cikin rashin aikin yi tare da haifar da danniya a kasuwar mai.
A ranar Lahadi, 15 ga wannan watan ne matatar ta sanar da fara rarraba Man fetur da Dizal kai-tsaye zuwa ga ‘yan kasuwa da dillalai da kuma sauran manyan kamfanoni daga ranar 15 ga Agusta, 2025 ba tare da karin kudi ba.
Kamfanin ya kara da cewa, ya sayo sababbin manyan motocin daukar mai 4,000 da ke aiki da iskar gas na CNG tare da samar da damar karbar Mai bashi ga wadanda za su saya kan lita 500,000 zuwa sama .
Sai dai wannan ci gaba ya haddasa zazzafar suka daga masu gidajen mai da masu motocin dakon mai, wadanda suka ce tsarin zai durkusar da ayyukansu da kuma kawar da damar cinikayyar da suke da ita da manyan kamfanoni.
Kungiyar PETROAN ta bukaci hukumomin da abin ya shafa da su sa baki domin hana matatar Dangote aiwatar da aniyarta. Wanda matatar ta ce, hakan zai taimaka wajen rage tsadar Mai a kasa da wahalhalun da sayensa ya janyo wa jama’ar kasar.