
Jami’an ’yan sanda a jihar Binuwai sun kama mutane biyar da ake zargi da hannu a kisan wasu matasa biyu ’yan asalin jihar Kano a garin Agan da ke kusa da Makurdi.
Mai Magana Da Yawun Gwamnan Binuwai, Sir Tersoo Kula, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata
Kakakin gwamnan ya bayyana cewa kama wadannan da ake zargi ya biyo bayan umarnin da gwamna Hyacinth Alia ya ba wa kwamishinan ’yan sanda da sauran jami’an tsaro na jihar ne a lallai a kamo masu hannu a cikin lamarin.
“Wannan kisa abin ƙyama ne da rashin imani” In ji shi. Ya kuma jaddada cewa sai an hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Gwamna Alia ya kuma miƙa sakon ta’aziyya ga gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma iyalan marigayan.
Ya kuma ce ‘yan sanda za su yi bincike dan gano wadanda suke da laifi a kisan dan ganin an hukuntasu.