Takaddamar ta kaure ne a majalisar dattawa yayin da Sanata Ali Ndume ya yi martani ga Mataimakin Shugaban Majalisar, Barau Jibrin kan kokarin gayyatar kwararru kan haraji da jami’an gwamnati zuwa zauren majalisa ba tare da sanarwa ba.
Rikicin ya ta’allaka ne kan Dokokin Gyaran Haraji, inda wasu ƴan majalisa daga yankin arewa suka bayyana rashin amincewarsu.
Sanata Barau Jibrin, wanda ke jagorantar zaman majalisar ya mayar da martani ta hanyar cewa dokokin gyaran haraji suna da muhimmanci ga kasa kuma tuni Majalisar Wakilai ta yi aiki a kansu.
Sanata Ndume, cikin bacin rai ya fada wa shugaban zaman majalisar kin amincewar al’aummar Arewa.
Rikicin ya kara ta’azzara lokacin da Sanata Ndume cikin takaici, ya jagoranci wasu ‘yan majalisa daga arewa wajen ficewa daga zaman majalisar a matsayin alamar rashin jin dadi game da take dokar majalisa.