Matar tsohon Gwamnan jihar Kano Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta ba mata uku da suka yi nasara a gasar Hikayata ta na BBC, kyautar Naira Miliyan hudu da rabi.
Dakta Hafsat wacce aka fi sani Gwaggo, ta yi wannan alkawari ne a jawabinta a yayin bikin karrama wadanda suka yi nasara a gasar ta shekarar 2024 wanda aka gudanar a Abuja a ranar Laraba.
Gwaggo ta ce za ta bai wa wacce ta zo ta ɗaya kyautar naira miliyan biyu. Ta biyu za ta samu kyautar naira miliyan ɗaya da rabi, sai kuma ta uku da za ta samu kyautar naira miliyan daya.
A gasar ta bana wata matashiya ce mai suna Hajara Ahmed Hussain ce daga jihar Jigawa ta zo ta daya
Hajara, ta sami lambar yabo da kuma kyautar naira 1,000,000 daga BBC.
Sai Amrah Umar Mashi da ta zo ta biyu a inda ta samu kyautar naira 750 da kuma Zainab Muhammad Chubado da ta samu kyautar naira 500,000.
Taron na wannan shekara ya samu harlartar manyan baki ciki har da gwamnan jihar Katsina Dikko Radda da Sanata Ali Ndume da Jakadan kasar Bulgariya a Najeriya da kuma Farfesa Abdallah Uba Adamu na Jami’ar Bayero.
Rayuwar wacce ta lashe gasar
Hajara wacce ta lashe gasar ‘yar asalin unguwar Kaburu a Hadeja ce, ta yi karatun arabiya da boko har zuwa matakin difloma a fannin lissafi, yanzu haka Hajara na da aure da yara.
Ta kuma kasance ma’abociyar karance-karance tun lokacin da take sakandire har zuwa lokacin da ta yi aure.
Ta kan yi rubutu a takarda da biro amma ba ta samu damar buga su ba har aka fara yi a yanar gizo a shekarar 2015 wanda ita ma ta fara yi a yanar gizo domin isar da sakonni masu yawa ga mutane.
Ya zuwa yanzu Hajara ta rubuta litattafai kusan 20 baya ga wasu gajerun labarai.