Jam’iyyar PDP na gudanar da wani babban taro a Jos babban birnin jihar Plato.
Taron na gudana ne a karkashin Jagorancin Bala Muhammad gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP na kasar nan.
Rahotanni na cewa, taron wani yunkuri ne na lalubo hanyoyin magance rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar adawa.
Gwamnan Adamawa Ahmadu Umar Fintiri da Kefas Agzu na Taraba da Dauda Lawal na Zamfara da Seyi Makinde na Oyu da Caleb Muftwang na Plateau da kuma Umar Damagun shugaban riko na PDP na kasa na cikin wadanda ke halartar taron