
Gwamnatin Taliban ta halarci taron majalisar ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi a karon farko tun bayan ƙarbe ragamar mulki a shekarar 2021.
Hukumar Kula da Kare Muhalli ta ƙasar ta sanar ta hakan a shafinta na X, tana mai cewa jami’anta sun halarci taron da ake gudanarwa a Baku da ke kasar Azarbajain
Kasar na halartara taron ne a matsayin ‘yar kallo a wajen taron.
An fara gudanar da taron na COP29 a ranar Litinin kuma ɗaya daga cikin muhimman tattaunawa da za a yi shi ne kan Taliban.
Matiul Haq Khalis, shugaban hukumar ta Afghanistan ya ce, tawagar za ta yi amfani da taron wajen karfafa haɗin kai da ƙasashen duniya kan kare muhalli da kuma rikicin sauyin yanayi.
Wasu kwararru a hirarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na AP sun ce, rikicin sauyin yanayi ya janyo illoli da yawa kan Afganistan saboda yankin da ƙasar take da kuma rashin ɗaukar kwararar matakan yaki da illar.
A watan Agusta, kungiyar agaji ta ƙasa da ƙasa ta ‘Save The Children’ ta fitar da wani rahoto da ke cewa Afganistan ce ƙasa ta shida a duniya mafi rauni da ke illatuwa da tasirin sauyin yanayi, kuma 25 daga lardunanta 34 na fuskantar matsanancin fari, wanda ke shafar sama da rabin jama’ar kasar.