
Jam’iyyar PDP ta sanar da cewa yankin kudu zai tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Wannan mataki ya fito ne daga taron majalisar zartarwa karo na 102 da aka gudanar a Abuja.
Haka kuma, jam’iyyar ta tabbatar da Umar Iliya Damagum a matsayin shugaban ƙasa na jam’iyyar a hukumance, bayan shafe fiye da shekara guda a matsayin shugaban riƙo.
Ana ci gaba da kiraye-kirayen tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, da ya tsaya takara, duk da cewa bai bayyana matsayinsa ba tukuna.