Gwamnonin jihohin Kudu-Maso-Yammacin Najeriya sun gudanar da babban taro na sirri a Ibadan.
A taron sun tattauna batutuwan tsaro da ci gaban yankin tare da kulla yarjejeniyar hadin Kai.
An gudanar da taron ne a sakatariyar jihar Oyo da ke Agodi.
Taron ya samu halartar dukkan gwamnonin yankin.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin Kudu-Maso-Yamma kuma Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ne ya jagoranci taron.
Sauran gwamnonin da suka halarta sun haɗa da Gwamnan jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa da Ademola Adeleke na Osun da Dapo Abiodun na Ogun da Biodun Oyebanji na Ekiti; da kuma Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde mai masaukin baki.
Rahotannin sun nuna cewa taron na da nasaba da tsanantar matsalolin tsaro da ke addabar yankin, musamman yadda ake ci gaba da samun hare-hare da satar mutane a wasu sassa na yankin.
Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnonin sun tattauna hanyoyin hanzarta aiwatar da muhimman aikace-aikacen more rayuwa da za su inganta tattalin arziki da rayuwar al’ummar yankin.
Haka kuma an yi nazari kan matakan ƙarfafa haɗin kai tsakanin jihohi domin inganta shirin raya yankin.
Gwamnonin sun kuma yi kudurin mayar da hankali kan sake duba yadda rundunar sa-kai ta yankin, wato Amotekun, ke gudanar da ayyukanta.
Za kuma su ƙara inganta rundunar da kayan aiki da dabaru da kuma horo domin fuskantar sabon salo da ƙalubalen tsaro da ke tasowa.
Ana sa ran za a fitar da cikakken bayanin taron a hukumance nan gaba kadan bayan kammala tattaunawa tsakaninsu.
