Sojojin Najeriya sun samu nasarar daƙile wani sabon yunƙurin kai hari da ake zargin wasu ‘ƴan bindiga ne suka shirya kai wa a wasu ƙauyuka da ke cikin ƙaramar hukumar Shanono.
A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar, Babatunde Zubairu ya fitar, ya ce, sojojin sun samu rahoton cewa an ga wasu ‘ƴan bindiga a ƙauyukan Unguwan Tudu da Unguwar Tsamiya da kuma Goron Dutse da misalin ƙarfe biyar na yamma, a ranar 1 ga Nuwamba, 2025.
Bayan samun wannan bayani, dakarun sojojin suka tunkari yankin tare da dakile shirin ƴan bindigar, lamarin da ya hana aukuwar hari da asarar rayuka ko dukiya.
Kwamandan sashen, Birgediya Janar Ahmed Tukur ya yaba wa mazauna yankin bisa haɗin kai da bayanan da suka bayar, yana mai kira gare su da su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.
Ya kuma bukace su da su riƙa kai rahoton duk wani motsi da suka lura da shi, domin taimakawa jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Janar Tukur ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da aiki tare da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da cewa Jihar Kano ta ci gaba da kasancewa cikin aminci da kwanciyar hankali.
