Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da dakatar da sayar da man fetur da naira, lamarin da ya tayar da hankulan ‘yan kasuwa tare da haifar da damuwa kan farashin mai da matsin tattalin arzikin musayar kudi.
A wata sanarwa da kamfanin ya tura wa abokan cinikin sa da misalin ƙarfe 6:42 na yamma a ranar Juma’a, ya bayyana cewa wannan mataki zai fara aiki daga Lahadi, 28 ga Satumba, 2025, bayan ƙarewar tsarin musayar mai da Naira.
Sanarwar wacce sashen harkokin kasuwanci na matatar Dangote ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa abokanan kasuwancin nasu da ke da ciniki a kan naira za su iya neman a mayar musu da kuɗin su.
Masana harkokin kasuwanci sun yi gargadin cewa sabon matakin na iya haifar da tashin farashin mai zuwa fiye da ₦900 kowacce lita, yayin da wasu suka nuna tsoron cewa hakan zai ƙara tsananta dogaro da dala a kasuwar mai.