Sarkin Musulmi Sir Abubakar Sa’ad na III ya roƙi gwamnatin jihar Sokoto da ta shigar da sarakunan gargajiya cikin tsarin biyan mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70
Sarkin musulmin wanda ya samu wakilcin Hakimin Wurno Sarkin Sudan Kabiru Ci Gari Al Hassan, ya yi roƙon ne a yayin taron Tattaunawa da al’umma wanda Ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare ta Jihar ta shirya, domin shirin mika kasafin kuɗin jihar na shekarar 2026.
Sarkin ya jaddada cewa sarakunan gargajiya suna goyon bayan aiwatar da dukkan manufofi da shirye-shiryen gwamnati a fadin jihar.
