
Agbamuche-Mbu za ta jagoranci hukumar har sai Shugaba Bola Tinubu ya naɗa sabon shugaba, wanda zai fuskanci tantancewar majalisar dattawa.
Wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya fara a 2015, ya zo ƙarshe, inda ya zama mutum na farko da ya yi wa’adi biyu a matsayin shugaban hukumar.
May Agbamuche-Mbu ita ce Kwamishiniyar ƙasa mafi daɗewa a INEC, wanda hakan ya sa ta cancanci a ba ta muƙamin shugabar riƙo. Za kuma ta jagoranci hukumar har sai Shugaba Bola Tinubu ya naɗa sabon shugaba, wanda majalisar dattawa za ta tantance.
Mai shari’a Agbamuche-Mbu ƙwararriyar lauya ce da ke da gogewar aiki sama da shekaru talatin a fannin shari’a, warware rikice-rikice, da kuma hidimar jama’a. Ta yi digirin farko a fannin shari’a a Jami’ar Ife (yanzu Jami’ar Obafemi Awolowo) a shekarar 1984. Ta kuma zama lauya a Ingila da Wales, kuma tana da digiri na biyu a fannin Kasuwanci da Shari’ar Kasuwanci.
Ta kuma yi aiki a kwamitin tantance ayyukan shugaban ƙasa tsakanin 2010 da 2011, da kuma kwamitin ministoci na tsarin aikin ma’adanai a shekarar 2016.