Gwamnonin jihohin Arewa 19 za su gudanar da wani muhimmin taro a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, domin tattauna matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
Mai ba wa Gwamnan Nasarawa shawara na musamman kan harkokin jama’a, Peter Ahemba ne ya bayyana cewa taron da za a yi a Kaduna zai samu halartar manyan sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban na Arewa.
Ahemba ya ce, sakamakon matsalolin tsaro da wasu jihohin Arewa ke fuskanta, gwamnatin Nasarawa ta ɗauki matakan gaggawa na shirya wannan taro domin yanke shawarar da za ta kare jihar daga duk wata barazanar tsaro.
Ya kuma yi kira ga ’yan ƙasa da su taka rawa wajen magance barazanar tsaro ta hanyar ba wa hukumomin tsaro bayanai kan mutanen da ake zargin na aikata laifi.
