Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargaɗi kan ɓullar cutar shawara, wato Yellow Fever, a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka takwas.
A cewar rahoton hukumar, an tabbatar da kamuwa da cutar ga mutane 67, yayin da 18 suka rasu tsakanin 1 ga Janairu zuwa 12 ga Oktoban 2026 a ƙasashen tara.
Ƙasashen sun haɗa da Najeriya, Burkina Faso, Kamaru, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Côte d’Ivoire, Ghana, Guinea, Laberiya da Togo.
WHO ta bayyana cewa an fi fuskantar matsalar a Burkina Faso, Côte d’Ivoire, Ghana da Laberiya, musamman a yankunan kan iyakoki.
Hukumar ta danganta haɗarin yaɗuwar cutar da sauye-sauyen muhalli, sare dazuzzuka, ayyukan haƙar ma’adanai, zirga-zirgar jama’a da ƙarancin rigakafi.
WHO ta ce tana haɗa kai da ƙasashen da abin ya shafa domin dakile yaɗuwar cutar.
