Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya buɗe sabuwar cibiyar kula da masu cutar sikila ta zamani, wadda gwamnatin sa ta samar a asibitin ƙwararru na Murtala, da ƙaddamar da wasu muhimman shirye-shiryen harkokin lafiya domin tabbatar da ingantaccen tsarin kula da marasa lafiya a faɗin jihar.
Da yake jawabi a wajen, Gwamna Abba ya ce sabuwar cibiyar za ta dinga baiwa masu fama da cutar ta sikila cikakkiyar kulawa kyauta, tare da zama wajen gudanar da bincike domin samar da sabbin hanyoyin magance cutar.
A yayin taron, gwamnan ya kuma ƙaddamar da rabon na’urorin auna ciwon hawan jini guda dubu 3 ga manyan ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa, domin gano cutar da wuri domin taimakawa masu fama da ita wajen kula da lafiyar su.
A nasa jawabin, kwamishinan lafiya na Kano Dr Abubakar Labaran Yusuf, ya ce kafa cibiyar kula da masu cutar sikilar wata shaida ce ta ƙudirin gwamnatin jihar na ƙarfafa harkokin kiwon lafiya da samar da kulawa ta musamman ga masu fama da cutar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf cewa shiri zai inganta rayuwar marasa lafiya tare da rage mace-macen da cutar ta hawan jini ke haifarwa, tare da yin kira ga al’ummar Kano da su dinga gwajin cutar akai-akai domin tabbatar da halin da lafiyar su take ciki.
