Wani jami’in Vigilante a unguwar Tsamiya da ke Brigade, cikin karamar hukumar Nasarawa a Kano, Idris Salisu, ya rasu bayan da wani matashi da ake zargi, Abubakar Buli, ya caka masa wuka a gefen cikinsa.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar, inda aka yi gaggawar kai marigayin asibiti, amma ya rasu kafin a kai ga ba shi cikakkiyar kulawa.
- Gwamnatin Kano ta shawarci mazauna jihar akan ciwon sikari
- An gano motar da aka sace a gidan Gwamnatin Kano
Kwamandan Vigilante na unguwar Tsamiya, Abdullahi Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an yi jana’izar marigayin bisa ka’idojin addinin Musulunci. Ya ce suna gudanar da aiki tare da jami’an tsaro domin tabbatar da an cafke wanda ake zargi da aikata laifin.
Ya kara da cewa rundunar Vigilante za ta ci gaba da kai rahoton duk wani bayani da zai taimaka wajen gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci.
