
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyana damuwarsa kan tabarbarewar da fannin shari’a ke fuskanta a Najeriya, yana mai zargin wasu manyan alƙalai da karɓar cin hanci da yanke hukunci bisa son rai, yana kiran su “baragurbi” dake lalata adalci.
El-Rufai ya yi wannan furuci ne a ranar Litinin yayin taron makon shari’a da Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta shirya a garin Bwari, babban birnin tarayya Abuja.
A cewarsa, “cin hanci da rashawa ya yi katutu a tsakanin manyan alƙalai,” yana mai jaddada cewa wannan lamari na kawo cikas ga zaman lafiya da cigaban ƙasa.
El-Rufai ya kuma bukaci Ƙungiyar Lauyoyi da ta tsaya tsayin daka wajen ganin an gyara fannin shari’a, domin dawo da martabar kotuna da kuma amincewar al’umma da tsarin shari’a a ƙasar.
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana rashin amincewarsa da batun ayyana dokar ta ɓaci a Jihar Ribas, yana mai cewa hakan “na iya zama ƙofa ga take hakkin jama’a da bin hanyoyi marasa tsari.”
El-Rufai ya yi kira da a samar da sauyi mai ma’ana cikin tsarin shari’a, yana mai cewa lokaci ya yi da Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya za ta tashi tsaye don kare gaskiya da doka.