Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya tabbatar wa da ƴan kasar nan cewa, gwamnatin sa na ci gaba da fito da sabbin hanyoyi domin magance matsalar tsaro a fadin ƙasar nan.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin da ya karɓar bakuncin Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya wato CAN karkashin jagorancin shugabanta Bishop Daniel Okoh, a gidansa da ke Legas a jiya Juma’a, kamar yadda da mai magana da yawun shugaban kasar wato Bayo Oyanuga ya fitar.
Shugaban Tinubu ya bayyana cewa, a shirye gwamnatinsa take wajen kirkiro da ƴan sandan jihohi domin inganta harkokin tsaro a fadin ƙasar nan.
Ya yi kira ga kungiyar ta CAN da ta yi aiki da gwamnatinsa domin cimma manufofin da aka sanya a gaba, inda ya ce wasu matakai da gwamnatinsa ta ɗauka na buƙatar lokaci kafin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
