Bankin duniya yace gwamnatin Tarayya ta raba tallafin kuɗi kai tsaye naira biliyan 658.9 ga iyalai matalauta da masu rauni miliyan 10.46, zuwa watan Satumbar 2026.
Sai dai bankin ya buƙaci gwamnati ta faɗaɗa shirin, ta ƙara adadin kuɗin tallafin da ake bayarwa, tare da tabbatar da cewa ana biyan waɗanda suka cancanta a kai a kai.
Bankin ya bayyana hakan ne cikin sabon rahotonsa mai taken *Beyond the Federal Purse: wanda ya yi nazari kan yanayin tattalin arzikin Najeriya da kuma matakan da gwamnati ke ɗauka domin rage wa jama’a raɗaɗin matsin tattalin arziki.
To ko me yan Najeriya ke cewa kan raba tallafin
Rahoton ya ce gwamnatin ta yi amfani da fasahar zamani wajen gano waɗanda suka cancanci tallafin da kuma aika musu da kuɗaɗen.
