Gwamnatin Kano ta ce al’ummar kwaryar birnin jihar za su samun ruwan famfo a watanni ukun Ƙarshen 2026, yayin da ake ci gaba da aikin gyara manyan tashoshin samar da ruwa na Challawa da Tamburawa.
Kwamishinan ma’aikatar muhalli, ruwa da sauyin yanayi Dr Dahiru Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar duba yadda aikin gyaran matatar ruwan Chalawa da rumbun ajiyar ruwa na goron dutse yake gudana.
Dr Dahiru ya ce gwamnati na shirin fara gwajin tsarin samar da ruwa a kwaryar birnin jihar domin tabbatar da yadda matatun da ake gyarawa za su yi aiki, inda ya ce aikin samar da ruwan yana tafiya ne daki-daki, saboda ba za’a iya magance matsalar baki daya lokaci guda ba.
Kwamishinan ya ce gwamnati za ta tabbatar da gyara duk wani muhimmin kayan aiki da ya lalace, domin hana sake faruwar matsalar karancin ruwa a fadin kano bayan kammala ayyukan gyaran.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Dahiru na tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da sanya ido kan aikin, domin tabbatar da cewa duk wanda ke da alaka da tsarin samar da ruwa ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata, tare da cika alkawarin samarwa al’ummar Kano wadataccen ruwan famfo.
