Rundunar ƴan sandan kasar nan ta kama wasu mutane biyu da ake zargin su da aikata laifukan fashin daji da kuma yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a jihohin Katsina da Zamfara da Neja da kuma Kwara.
An kama su ne a ranar 19 ga Disamba na wannan shekarar a jihar ta Kwara biyo bayan fadada aiyukan sintiri da jami’an yan sandan suka yi a jihohin guda hudu.
Daya daga cikin wadanda aka kama sun hadar da Abubakar Usman wanda aka fisanin shi da Siddi da kuma Shehu Mohammadu wanda rundunar yan sandan ta jima tana neman su ruwa ajallo bisa muggun aiyukan ta’addacin da suka gudunarwa.
- Mun Tsaurara Tsaro A Kan Iyayokin Kano – Rundunar ‘Yan Sanda
- Rundunar ‘Yansandan Jihar Neja, Ta Kashe Masu Garkuwa Da Mutane
- ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Da Harsasai 1,000 a Zamfara
Sanarwar yan sanda ta bayyana cewa, daga cikin kayayakin da aka kwato daga hannun matunan sun hadar da babur mai kafa biyu da kudi dubu fari 500,000 da bindiga kirar AK-47 da kuma harsashi 20.
Rundunar yan sandan ta kara da cewa, wadanda aka kama mambobi wata kungiyar ‘yan fashin daji ne da suka addabar jihohi da dama musamman a Arewacin kasar nan wajan kai hari da muggun makamai.
