Mayaƙan RSF sun amince da shiga yarjejeniyar tsagaita wuta ta watanni uku a yaƙin Sudan, domin bayar da damar shigar da kayayyakin agaji, yayin da dakarun gwamnati suka ƙi amincewa da hakan.
Shugabannin ƙungiyar RSF a Sudan sun sanar a jiya Litinin cewa sun amince da shiga yarjejeniyar tsagaita wuta a a yaƙin Sudan, bayan shugaban Amurka Donald Trump a makon da ya gabata ya ce zai shiga tsakani don kawo ƙarshen rikicin.
Ƙasashen Amurka da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Masar da kuma Saudi Arabia da aka fi sani da Quad, su ne suka gabatar da shirin tsagaita wutar na watanni 3, biyo bayan tattaunawar zaman lafiya da aka gudanar.
To sai dai jim kaɗan bayan RSF ta sanar da amincewa da yarjejeniyar, ta ƙaddamar da harin jirgi maras matuƙa a kan sansananin sojin Sudan.
Wannan na zuwa ne kwana guda, bayan dakarun gwamnatin ƙasar sun ƙi amincewa da tsagaita wutar, inda ta caccaki sanya Daular Larabawa cikin masu shiga tsakanin, ganin yadda aka jima ana zarginta da goyawa mayaƙan RSF baya, koda yake Daular Larabawar ta yi watsi da zargin har ma ta ce ba ta da burin da ya wuce a kawo ƙarshen yaƙin na Sudan.
