Kwamitin tsarin mulkin na Ghana, ya bayar da shawarar mayar da shekarun da shugaba zai yi yana mulki zuwa biyar, maimakon huɗu da ake yi yanzu haka.
Kwamitin da shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahama ya kafa don yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyaran fuska, ya kammala aikinsa, tare da gabatar da rahoto ga gwamnati.
Kwamitin ya bayar da shawarar mayar da shekarun da shugaba zai yi yana mulki zuwa biyar, maimakon huɗu da ake yi yanzu haka.
A baya-bayan nan ne dai muhawara ta ɓarke a cikin ƙasar kan yiwuwar shugaba Mahama ya tsaya takara a karo na uku, duk da cewa kundin tsarin mulkin ƙasa wa’adi biyu ya bai wa kowane shugaban ƙasa damar ya yi na shekaru huɗu-huɗu.
Ganin cewa sai da Mahama ya yi wa’adinsa na farko, kana ya sha kaye a zaɓe, kafin daga bisani ya sake ɗarewar karagar mulki bayan shekaru hudu, ake ganin yana iya samun damar sake yin takarar a karo na uku.
A cewar shugaban kwamitin, Farfesa Kwasi Prempeh, babu wani sashe da ya halastawa shugaba Mahama tsayawa takara a karo na uku.
Prempeh ya kuma ce, dama babu wanda ya buƙaci a bijiro da tsarin yin wa’adi uku na shugabanci a Ghana, a don haka baya cikin irin gyare-gyaren da su ka yi.
