
Hukumar Kula da Birnin Tarayya Abuja (FCTA) ta bayar da wa’adin kwanaki 14 ga masu filaye da gidaje 4,794 a birnin da suka kasa biyan haraji da gaggauta yin hakan.
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Ezenwo Wike ne ya bayyana cewa, sabon tsarin zai shafi masu filaye da kadarori da ke tsakiyar Abuja, inda aka nemi su biya harajin Naira miliyan 5, tare da bashin da ake binsu a baya.
A cewar ministan, masu kadarorin dake a unguwannin Maitama da Asokoro da Wuse II da Guzape za su biya harajin Naira miliyan 3, yayin da masu filaye da ke unguwannin Wuse I da Garki I da Garki II an dora musu biyan Naira miliyan 2 a kowacce shekara.
Wike ya ce, wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnati na tabbatar da kiyaye dokokin biyan haraji, da kuma tafiyar da filaye yadda ya dace.
Hukumar FCTA ta bayyana cewa ana sa ran masu filayen za su bi wannan umarni tare da daukar matakin biyan bashin da ake binsu, domin kauce wa daukar matakan hukuma.