Babban Daraktan Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Najeriya (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi, ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin bunƙasa tattalin arzikin zamani a ƙasar.
Kashifu ya bayyana hakan ne yayin taron Global Tech Africa 2026 da aka gudanar a Kano, inda ya ce samar da ƙwararrun matasa, tallafa wa masu ƙirƙira da faɗaɗa hanyoyin sadarwar intanet na da muhimmanci wajen ci gaban Najeriya.
Ya bayyana cewa NITDA na haɗa kai da wasu hukumomi domin kafa asusun tallafi guda shida ga sabbin kamfanonin fasaha, tare da buƙatar masu zuba jari su ƙara tallafa wa wannan fanni.
Shugaban NITDA ya kuma jaddada buƙatar Najeriya ta bunƙasa fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI) da za ta fahimci harsunan gida da al’adun ƙasar.
Ya ce amfani da fasahar zamani wajen kasuwanci zai iya taimaka wa Kano wajen dawo da martabarta a matsayin babbar cibiyar kasuwanci a Afirka.
