
Ƙungiyar Likitocin Idanu ta Najeriya (OSN) ta gudanar da babban taronta na shekara-shekara, wanda ya haɗa da 49th Scientific Conference, a karon farko a birnin Kano.
Taron ya haɗa kwararru da masu ruwa da tsaki a fannin kula da lafiyar ido daga sassa daban-daban na ƙasa da ƙasashen waje.
A yayin taron, kungiyar ta rantsar da sabbin mambobi 48 a matsayin cikakkun likitocin ido.
Shugaban ƙungiyar, Dr. Umar Faruk Ibrahim, ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko da aka gudanar da taron a Kano, wanda zai taimaka wajen magance matsalolin ido da al’umma ke fuskanta.
Ya kara da cewa ƙungiyar na ƙoƙari sosai wajen yaki da likitocin bogi a bangaren ido, duba da yadda ake samun matsaloli wajen gudanar da aikin.
Haka kuma, kungiyar ta gudanar da aikin ido kyauta ga mutane 500 a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, tare da gabatar da makaloli da bajakolin injinan duba lafiyar ido.