Jam’iyyar PDP ta mayar da martani ga tsohon gwamnan jigawa sule lamido
kan barazanarsa na kai jam’iyyar kara Kotu bisa zargin hana shi takardar shiga takara.
Mataimakin mai magana da yawun jam’iyyar na kasa Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana haka a Abuja.
“Sule Lamido Wadata Plaza ya je, a maimakon Legacy House, inda ake sayar da fom a hukumance, kokarin kirkirar hayaniya ce kawai don jawo hankalin jama’a”. In ji shi.
Jami’in ya kuma ce, jam’iyyar na da niyyar ci gaba da gyara matsalolinta duk da kokarin da wasu ke yi na kawo cikas.
Ya kuma kara da cewa, PDP ba za ta bari wasu masu neman rigima su kawo tangarda ga shirye-shiryen gudanar da babban taron jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a Ibadan dake jihar Oyo, cikin watan Nuwamban 2025 ba.
Abdullahi ya kuma bayyana cewa zaɓen Tanimu Turaki a matsayin ɗan takarar maslaha na shugabancin jam’iyya, ya biyo tsarin tarihi da PDP ke bi, inda gwamnoni da manyan jiga-jigan jam’iyya ke yanke hukunci tare.
Tsohon gwamnan Sule Lamido, ya yi barazanar ne bayan ya kasa sayen fom din takarar kujerar shugaban jam’iyyar na kasa.
