Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na gab da fara zaman muhawara kan ƙaruwar tashin hankali tsakanin Amurka da Venezuela.
Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela ne ya buƙaci muhawarar domin tattauna takalar faɗan da Amurka ke yi wa kasarsa.
Rasha ta nuna cikakken goyon baya ga Venezuela, tare da nuna matukar damuwa kan matakan da Washington ke dauka da ta ke fakewa da na yaƙi da safarar muggan kwayoyi ne.
Amurka dai ta sanar da hana tankokin mai na Venzuela wucewa ta tekun ta, da cewa za ta kwace man ta kuma saida shi.
A nata bangaren Venezuela ta zargi Washington da fashi a tekun kasa da kasa.
