Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabon uban jami’ar ne yayin bikin yaye ɗaliban da suka kammala makarantar daga 2018 zuwa 2024 wanda ya gudanar a sabon dakin taro na Convocation Arena dake Jami’ar.
A kwanakin baya ne gwamnan ya sanar da naɗa Sarkin na lafiya mai shari’a Sidi Muhammad Bage a matsayin sabon uban jami’ar.
Bayan wannan Jami’ar ta bayar da digirin girmamawa ga wasu mutane biyar, bisa irin kwazo da suke nunawa wajen tallafawa jami’ar, cikinsu har da Marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata da tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.
Sauran sun haɗar da Hajiya Mariya Sunusi Ɗantata, mahaifiya ga attajiri Alhaji Aliko Dangote, sai Alhaji Aliyu Sa’idu Bebeji, sai kuma Alhaji Yahaya Mai kifi.
Wakilinmu Ibrahim Hassan Baƙo Ɗambatta ya ruwaito mana cewa taron ya samu halartar sarakunan gargajiya Hudu wanda suka hadar da mai martaba sarkin Kano Muhammad Sunusu II da sarkin Karaye, da sarkin Nassarawa lafiya, da ma sarkin Lafiyar Bare-Bari Alhaji Sidi Muhammad Bage.
