Gwamnatin Kano ta jaddada kudurinta na rage talauci ga al’ummar jihar ta hanyar karfafa fannoni daban-daban da kuma aiwatar da shirye-shiryen raya ƙasa masu ɗorewa.
Mataimakin Gwamnan Kano Alhaji Murtala Sule Garo, ne ya bayyana hakan, yayin babban taron tattaunawar da na jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya suka shirya kan hanyoyin rage talauci, wanda UNICEF da tarayyar turai suka shirya.
Garo ya ce talauci na ci gaba da zama babban ƙalubale a yankin arewacin Najeriya ta hanyoyi daban daban, wanda hakan yake shafar miliyoyin al’umma ta fuskar ilimi, kiwon lafiya, abinci mai gina jiki da damar tattalin arziki, yana mai cewa rage shi na buƙatar haɗin kai da jajircewar shugabanni da masu ruwa da tsaki.
Garo ya bayyana cewa gwamnatin Kano na ci gaba da bada fifiko ga shirye-shiryen ilimi, kiwon lafiya, ƙarfafa matasa da mata, da sauran ayyukan jin daɗin al’umma domin inganta rayuwar jama’a da bunƙasa tattalin arziki.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Garo na yabawa UNICEF da tarayyar turai bisa goyon bayan da suke bayarwa, tare da tabbatar da cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da haɗa kai da kungiyoyi masu zaman kansu ƙasa wajen aiwatar da manufofin da za su rage talauci da inganta rayuwar al’umma.
