Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS ko CEDEAO ta amince da ficewar kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso a matsayin mambobi daga ranar 29 ga watan Janairun 2025.
Ta kuma ayyana wa’adin mika mulki na watanni shida har zuwa watan Yulin 2025.
Shugaban hukumar ECOWAS Dakta Omar Touray ne ya bayyana hakan a wajen rufe taro na 66 na shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS suka gudanar.ungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS ko CEDEAO ta amince da ficewar kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso a matsayin mambobi daga ranar 29 ga watan Janairun 2025.
Ta kuma ayyana wa’adin mika mulki na watanni shida har zuwa watan Yulin 2025.
Shugaban hukumar ECOWAS Dakta Omar Touray ne ya bayyana hakan a wajen rufe taro na 66 na shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS suka gudanar.
Touray ya ce, Hukumar ta lura da bukatar Burkina Faso da Mali da Nijar na janyewa daga kungiyar, saboda haka bisa ka’ida ta 91 na yarjejeniyar ECOWAS, kasashen uku za su daina zama mambobin ECOWAS daga karshen watan Janairun 2025.
A watan Janairun shekarar 2024, kasashen uku suka bayyana matakinsu na ficewa daga kungiyar bayan wasu jerin jutyin mulki da sojojin kasashen suka yi gwamnatocinsu na farar hula.
Sojojin Mali sun yi juyin mulki ne a shekarar 2020 da 2021, Burkina Faso a shekarar 2022 sai kuma Nijar a 2023.