Babbar kotun jihar Kano da ke kan titin Miller Road ta wanke tare da sallamar wani direban Adaidaita Sahu, Imran Mustapha, daga zargin kisan kai.
Mai shari’a Adam Abdullahi ne ya jagoranci shari’ar, inda ya yanke hukuncin cewa an wanke Mustapha bayan kotun ta gano cewa ba a tabbatar da laifin da ake zarginsa da shi ba.
Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Mustapha ne bisa zargin kisan kai, ƙarƙashin Sashe na 221 na Kundin Dokokin Penal Code. Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
A yayin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu shida domin tabbatar da zargin, yayin da lauyan kariya, Barrista Mubarak, ya gabatar da wanda ake tuhumar domin ya ba da nasa shaidar.
Shari’ar ta samo asali ne daga zargin cewa Mustapha ya bugi motar marigayi Alhaji Muhammad Mustapha a wani gidan mai.
Bayan faruwar lamarin, rahotanni sun ce marigayin ya bi motar Mustapha, lamarin da ya haifar da gardama tsakaninsu.
Masu gabatar da ƙara sun zargi Mustapha da sake bugun Muhammad Mustapha da motarsa, wanda suka ce hakan ya yi sanadin mutuwarsa.
Sai dai bayan nazarin hujjoji da bayanan da bangarorin biyu suka gabatar, kotun ta bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun kasa tabbatar da zargin kisan kai yadda doka ta tanada.
Saboda haka, Mai shari’a Adam Abdullahi ya wanke Imran Mustapha tare da sallamarsa daga tuhumar kisan kai.
Bayan hukuncin, lauyan gwamnatin jihar, Barrista Usman Abdullahi, ya bayyana cewa gwamnati ba ta gamsu da hukuncin ba.
Ya ce gwamnati za ta ɗaukaka ƙarar zuwa wata babbar kotu domin neman sake duba hukuncin.
