
Jam’iyyar APC ta musanta rahotannin da ke cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na shirin sauya Mataimakinsa Kashim Shettima kafin zaɓen 2027.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Ƙasa Alhaji Bala Ibrahim ya fitar ya ce, babu wata matsala tsakanin Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa, kuma jita-jitar da ake yaɗawa ba ta da tushe.
“Wannan jita-jita ce kawai da wasu ke yaɗawa domin tayar da ƙura. Babu wani sabani ko matsala da ke tsakanin Shugaba Tinubu da Mataimakin sa,” In ji Bala Ibrahim.
Ya ƙara da cewa, ko da a ce akwai wani dalili da zai sa Shugaban Ƙasa ya sauya mataimakinsa, ba zai iya yin hakan shi kaɗai ba.
Sai dole ya yi shawarwari tare da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar kafin a yanke irin wannan muhimmiyar shawara.
APC ta jaddada cewa gwamnatinsu na aiki kafada da kafada don tabbatar da ci gaban ƙasa, kuma irin waɗannan jita-jita ba za su hana su aiwatar da ajandar da suka ɗora a gaba ba.