Gwamnatin Jihar Filato ta bada umarnin rufe dukkanin makarantun firamare da kuma sakandare a jihar saboda dalilan tsaro.
Wannan na cikin sanarwar da hukumar Ilimin Bai daya ta Jihar Filato ta fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa makarantun kwana za su rufe daga yau Asabar 22 ga Nuwamba 2025, yayin da makarantun jeka ka dawo za su rufe daga ranar Litinin 24 ga Nuwamba 2025.
- Gwamnatin jihar Filato ta dakatar da hakar ma’adanai
- An Kashe mutane 3 an jijkkata 2 a gonakin su a Filato
Hukumar ilimin bai dayan ta ce wannan matakin na da wucin gadi ne domin kare rayuwar dalibai da kuma tabbatar da kwanciyar hankalin al’ummar jihar.
Sanarwar ta bukaci hukumomin ilimi na ƙananan hukumomi, shugabannin makarantun da kuma shugabannin al’umma su bi umarnin tare da kasancewa cikin shiri da lura da yanayin tsaro a yankunansu.
