
Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa kofar jam’iyyarsu na buɗe don haɗin gwiwa muddin manufar haɗin gwiwar za ta kasance kan inganta rayuwar talaka ne.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC a garin Kano, jim kaɗan bayan kammala taron bikin murnar cikarsa shekaru 69 a duniya ranar Laraba.
“Yanzu haka jam’iyyar NNPP na ci gaba da nazari da tattaunawa da wasu manyan jam’iyyun siyasa domin ganin sun samar da tsari mai karɓuwa wanda zai taimaka wa rayuwar talakan kasar nan ta ko wacce fuska.
“Mu a NNPP ba mu rufe ƙofa ba. Za mu iya yin aiki da kowace jam’iyya muddin an fahimci cewa manufarmu ɗaya ce, ta taimakon talaka,” in ji Kwankwaso.
Tsohon Gwamnan ya kuma yi watsi da jita-jitar da ke yawo cewa shi ne ke juya gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa gwamnan na da cikakken ‘yancin gudanar da harkokinsa.
Kwankwaso ya kuma bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta kammala shirin farawa da tsare-tsaren tunkarar babban zaben 2027.