
Ahmad Hamisu Gwale
Yau Juma’a 22 ga Agustan 2025, za a fara sabuwar gasar Firimiyar Najeriya NPFL ta kasar wasannin shekarar 2025/2026.
Kungiyoyi 20 daga jihohin kasar daban-daban, sune za su fafata a gasar wadda ke zama karo na 54, kuma ta 36 tun bayan kwaskwarima zuwa babbar gasa a Najeriya.
Remo Stars itace ta lashe a bara, kuma za ta yi yunkurin kare kambunta a wasa da Rivers United a yau Juma’a kuma shi ne wasan farko na bana.
A gefe guda tun 2019 ansamu kungiyoyi hudu masu zaman kansu da za su buga gasar a bana, wato Remo Stars, Ikorodu City, Barau FC, da kuma Kun Khalifat.
Ga jerin kungiyo 20 da sunayensu, jihohinsu da kuma filayen wasannin da zasu buga gasar ta bana.
A jihar Abia akwai kungiyo biyu wato
- Abia Warriors FC mai filin was ana Umuahia Township Stadium
- Enyimba FC mai filin was ana Enyimba Stadium, Aba
Sai jiher Bauchi
- Wikki Tourists FC a filin ATB Stadium, Bauchi
Da kuma jihar Bayelsa
- Bayelsa United Football Club mai filin wasa na Samson Siasia Stadium, Yenegoa
A jihar Borno
- El Kanemi Warriors FC – El Kanemi stadium Maidugiri
Jihar Delta
- Warri Wolves FC Stephen Keshi Stadium, Asaba
Jihar Edo
- Bendel Insurance FC – Samuel Ogbemudia Stadium, Benin City
Akwai jihar Enugu
- Rangers International F.C – Nnamdi Azikiwe Stadium (The Cathedral), Enugu
Da jihar Imo
- Kun khalifat – Dan Anyiam Stadium Owerri
A jerin akwai jihar Kano mai kungoyoyi biyu a karon farko da za a samu damar ganinsu a gasa daya.
- Barau Football Club – Sani Abacha Stadium, Kano
- Kano Pillars – Sani Abacha Stadium, Kano State
Katsina
- Katsina United – Muhammadu Dikko Stadium, Katsina
Kwara
- Kwara United – Rashidi Yekini Mainbowl, George Innih Stadium, Katsina
Lagos
- Ikorodu City FC – Mobolaji Johnson Arena, Onikan
Nassarawa
- Nasarawa United – Lafia City Stadium
Niger
- Niger Tornadoes FC, Minna – Ahmadu Bello Stadium, Kaduna
Ogun
- Remo Stars Sports Club – MKO Abiola Sports Arena, Kuto Abeokuta/ Remo Stars Stadium Ikenne
Oyo State
- 3SC Shooting Stars Sports Club – Lekan Salami Stadium Ibadan
Plateau State
- Plateau United FC – New Jos Stadium, Zaria Road
Rivers State
- Rivers United F. C. – Adokiye Amiesimaka Stadium Port Harcourt
Ga jerin wasanni mako na farko da za su gudana.
Remo Stars da Rivers United
Abia Warriors da Kano Pillars
Wikki Tourists da Plateau United
Katsina United da Warri Wolves
Rangers International da Kun-Khalifat
Kwara United da Ikorodu City
El-Kanemi Warriors da Bendel Insurance
Shooting Stars da Bayelsa United
Barau FC da Enyimba International
Niger Tornadoes da Nasarawa United