Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin dake matsalar tsaro, da suyi sulhu da ‘yan ta’dda da ‘yan bindigar dake cikin su ko kuma su yi amfani da karfin soji da gaske wajen kawo karshen su.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wajen taron kaddamar da rundunar tsaron unguwannin Kano ta Neighbourhood watch a filin wasa na kofar mata.
Kwankwaso ya kuma zargi gwamnatin tarayya da gaza yin abinda ya dace musamman ta bangaren tallafawa yunmurin sojin Najeriya na shawo kan matsalar tsaron inda yace matsalar dake damun wasu daga cikin arewacin Najeriya matsala ce babba wadda take bukatar daukar dukkan matakan da suka dace domin kawo karshen ta.
Kwankwaso ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara adadin jami’anta sojin ta ya zuwa miliyan 1 domin tunkarar matsalar tsaron, musamman ta hanyar mayar da jami’ar tsaron gwamnonin jihohin kasar suka dauka aiki dan kare iyakokin su ya zuwa jami’an soji.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Kwankwaso na bukatar Shugaban kasa Bola Tinubu da ya kwashe jami’an tsaron dake gidan Sarki na Nasarawa tare da baza su ya zuwa sassa Najeriya dake fama da matsalar tsaro.
