Rundunar yan Sandan Jihar Zamfara, ta tabbatar da fashewar wani bam a kan hanyar Dan sadau zuwa Magami, alamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu matafiya.
Kakakin rundunar yan sandan jihar ta Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar alamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya kara da cewa, lamarin ya faru ne a jiya Asabar da misalin ƙarfe 2:30 na rana da ke Ƙaramar Hukumar Maru.
- Ƴan sanda sun kama masu garkuwa da mutane da ake addabar jihohin Zamfara, Katsina, Kwara
- Yan Siyasa Na Shirin Kai Ganduje Kara Kan Hisbah Mai Zaman Kanta
Sanarwar ta ƙara da cewa fashewar ta lalata wata mota, tare da hallaka wasu mutane, ciki har da wani babur da ke kusa da wajen lokacin da lamarin ya faru.
Kakakin rundunar yan sandan ya ƙara da cewa, tuni aka fara gudunar da bincike kan musabbabin lamarin, yayin da ƙwararru da sauran sassan da abin ya shafa ke wajen domin tantance halin da ake ciki.
Rundunar ta yi kira ga al’umma da su kasance cikin natsuwa, su yi taka-tsantsan, tare da kai rahoton duk wani abun zargi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa ko wata hukuma ta tsaro.
