Yau ce ranar Kirsimeti, inda sama da kiristoci milyan dubu biyu a duk faɗin duniyar nan ke bikin tunawa da haihuwar Yesu Kiristi da aka yi a garin Bethlehem, da ke kudu da birnin Qudus.
Sama da shekaru dubu biyu ke nan mabiya addinin suka kwashe su na wannan biki ta hanyar nuna farin ciki, da ƙauna, da tausayin juna, da sadaukarwa, da dai sauransu.
A Bethleham, mahaifar Yesu Kiristi, da ke cikin kasar Falasɗinu, daruruwan mutane na kai ziyara a irin wannan lokaci a shekarun baya.
Amma a bana yankin ya kasance shiru, sai dai da dama sun mayar da hankali ne wajen yi wa waɗanda hare-haren Isra’ila ya hallaka a yankin Gaza addu’a.
A jawabin da Fafaroma Francis ya gabatar a majami’ar Saint Peter’s Basilica yayin taron jajibirin Kirsimeti a jiya, ya ja hankalin kiristoci su yi tunani game da yaƙe-yaƙen da ake fama da su a sassan duniya, yayin da a bana ma ake gudanar da bukukuwan cikin yaƙi tsakanin Isra’ila da Hamas, da kuma Rasha da Ukraine.
Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da ya yi tir da mummunan hare-haren da Isra’ila ke kai wa, wanda jami’an diflomasiyyar Isra’ila suka yi watsi da su.Kirismeti: Kiristoci sama da biliyan 2 na bikin tunawa da haihuwar Yesu Kiristi
Yau ce ranar Kirsimeti, inda sama da kiristoci milyan dubu biyu a duk faɗin duniyar nan ke bikin tunawa da haihuwar Yesu Kiristi da aka yi a garin Bethlehem, da ke kudu da birnin Qudus.
Sama da shekaru dubu biyu ke nan mabiya addinin suka kwashe su na wannan biki ta hanyar nuna farin ciki, da ƙauna, da tausayin juna, da sadaukarwa, da dai sauransu.
A Bethleham, mahaifar Yesu Kiristi, da ke cikin kasar Falasɗinu, daruruwan mutane na kai ziyara a irin wannan lokaci a shekarun baya.
Amma a bana yankin ya kasance shiru, sai dai da dama sun mayar da hankali ne wajen yi wa waɗanda hare-haren Isra’ila ya hallaka a yankin Gaza addu’a.
A jawabin da Fafaroma Francis ya gabatar a majami’ar Saint Peter’s Basilica yayin taron jajibirin Kirsimeti a jiya, ya ja hankalin kiristoci su yi tunani game da yaƙe-yaƙen da ake fama da su a sassan duniya, yayin da a bana ma ake gudanar da bukukuwan cikin yaƙi tsakanin Isra’ila da Hamas, da kuma Rasha da Ukraine.
Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da ya yi tir da mummunan hare-haren da Isra’ila ke kai wa, wanda jami’an diflomasiyyar Isra’ila suka yi watsi da su.