Gwamnatin Kano ta musanta rahoton da jaridar Daily Nigerian ta wallafa, wanda ta yi zargin cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya dakatar da karbar takardun aiki daga hukumomi da ma’aikatun jihar, wanda hakan zai janyo tsaiko da durƙusar da harkokin gudanar da gwamnati.
Cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin jihar, Umar Faruk Ibrahim, ya sanyawa hannu, gwamnatin ta bayyana rahoton a matsayin na ƙarya kuma mai kokarin ruɗar da mutane.
Sanarwar ta bayyana cewa an bayar da umarnin ne a ƙarshen watan Disamba shekarar da ta gabata, lokacin da dokar kasafin kuɗin shekarar 2025 ya ƙare, yayin da sabon kasafin kuɗin ya ke jiran sahalewar majalisar dokokin jihar, sabanin rahoton jaridar da ya ce an bayar da umarnin ne a zaman majalisar zartarwar jihar da ya gudana a karshen makon nan.
- Gwamnan Kano Ya Taya Premier Radio Murnar Cika Shekaru 4
- Gwamnatin Kano Za Ta Tallafawa Matasa Ta Hanyar Sana’o’in Dogaro da Kai a 2026
- Gwamnatin Kano Ta Biya Naira Biliyan 2 Don Karɓo Takardun Daliban Lafiya a Cyprus
Gwamnatin ta ce manufar umarnin a wancan lokacin, an yi ne ba don a tsayar da harkokin mulki ba, sai dai don a tabbatar da ɗa’a da tsari a harkokin kuɗi, inda gwamnati ta bayyana matakin a matsayin ingantacce wanda aka ɗauka domin hana kashe kuɗaɗe ba tare da izini ba.
Wakilinmu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, gwamnatin ta kuma tabbatar wa al’umma cewa ayyukan gwamnati sun ci gaba ba tare da katsewa ba, inda ta ce muhimman ayyuka a fannonin tsaro, lafiya, ilimi da tsafta sun ci gaba da aiki yadda ya kamata bisa tanade-tanaden doka.
