
Fadar gwamnatin Rasha a Kremlin, ta mayar da martani mai ƙarfi kan sabbin kalaman da tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi dangane da yaƙin Ukraine, inda ta bayyana su a matsayin rashin fahimta da kuma sauyin matsayi da ba a amince da shi ba.
Donald Trump, yayin wata ganawa da ya yi da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, a gefen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ake yi a yanzu a birnin New York ya ce, Ukraine na da damar kwato duk yankunan da Rasha ta mamaye.
Ya kuma kwatanta Rasha da “kyanwar Lami”, wani abu da ke nuni da raunin ƙasar a fannin siyasa da tattalin arziki.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa Dmitry Peskov ya ce, “Rasha zakanyar ƙasa ce, ba kyanwar Lami ba kamar yadda ake ƙoƙarin nunawa.”
A cewarsa, “Babban kuskure ne a tunanin cewa Ukraine za ta iya kwato yankunan da ke karkashin ikon Rasha.