Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta jihar Kano (KNCDC) ta gargadi alumma da su sanya ido kan cutar zazzabin Dange da ta bulla.
Gargadin na cikin wata sanarwa da Darakta Janar na hukumar Dakta Muhammad Adamu Abbas ya fitar a ranar Litinin.
Ya ce ko da yake an samu bullar cutar ne a jihar Sokoto amma akwai bukatar al’umma su sanya ido tare da daukar matakan kariya duba da mu’amila da tafiye-tafiye da ake samu tsakanin jihohin.
Ya kara da cewa sauro ne ke yada nau’in zazzabin na Dange kuma alamominta su ne zazzabi mai zafi, da ciwon kai mai tsanani da kaikayin fatar ido.
Sauran alamomin sune ciwon gabobi da amai da borin jini.
Dakta Muhammad Adamu Abbas, ya kara da cewa babu maganin cutar zuwa yanzu amma daukar matakan lafiya da wuri na taimakawa wajen rage hatsarin kamuwa da ita.
Ya ce hukumar KNCDC ta dauki matakai a sassan kula da lafiya na jihar Kano da kananan hukumomi domin bibiya da daukar matakan kare yaduwar cutar a Kano.
Dakta Muhammad ya shawarci al’umma da su kula da magudanan ruwan da shiga gidan sauro tare da tuntubar likitoci.
Ya kuma bukaci mutane da su sanar da hukumar duk wata alamar bakuwar cuta.
